Siyasa

Abba Kabir Yusuf Ya Jinjinawa INEC Kan Zaɓen Cike Gurbi data gudanar

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yaba wa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) da kuma hukumomin tsaro bisa yadda suka tabbatar da gudanar da zaɓen cike gurbi cikin kwanciyar hankali da tsari a Jihar Kano.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Asabar.

 

Gwamnan ya bayyana zaɓen a matsayin wani muhimmin mataki a tafiyar dimokuraɗiyyar jihar, yana mai cewa yanayin zaman lafiya da aka samu a rumfunan zaɓe ya nuna yadda al’ummar Kano ke ƙara fahimtar muhimmancin siyasa mai tsafta.

 

Ya ce hakan ya samo asali ne daga ingantattun shirye-shiryen tsaro da aka shimfiɗa kafin da lokacin zaɓen.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button