Gwamnatin Tarayya Ta Gargaɗi ’Yan Kasuwa Kan Ɓoye Kaya da Tashin Farashi a Ramadan

Hukumar Wayar da Kai ta Ƙasa (National Orientation Agency) ta gargaɗi ’yan kasuwa da su guji ɓoye kayan abinci ko ƙara farashi ba bisa ƙa’ida ba yayin azumin watan Ramadan.
A wata sanarwa da Babban Daraktan hukumar, Lanre Issa-Onilu, ya fitar a ranar Alhamis, ya bayyana cewa sun samu rahotanni kan yadda wasu ’yan kasuwa ke ɓoye muhimman kayan masarufi domin haifar da ƙaranci a kasuwa, lamarin da ke haddasa tashin farashi.
Ya ce irin wannan dabi’a na kawo tangarda ga tattalin arziki, tare da jefa al’umma cikin wahala, musamman a wannan lokaci da addinai ke koyar da tausayi, sadaukarwa da taimakon juna.
Shugaban NOA ya ƙara da cewa ɓoye kaya da gangan na kawo cikas ga ƙoƙarin da ake yi na daidaita tattalin arziki, tare da ƙara wa iyalai nauyi a lokacin da suke fuskantar ƙalubalen rayuwa.



