Kwamishinan Yaɗa Labarai na Kano Ya Tattauna da Ƙungiyoyin Fararen Hula Kan Ci gaban Jiha

Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya jagoranci wani muhimmin taro da ƙungiyoyin fararen hula domin tattauna muhimman batutuwan da suka shafi ci gaban jihar tare da ƙarfafa haɗin gwiwa da gwamnati.
A yayin taron, kwamishinan ya yi wa mahalarta bayani kan shirye-shiryen da gwamnatin Abba Kabir Yusuf ke aiwatarwa, inda ya jaddada muhimmiyar rawar da ƙungiyoyin fararen hula ke takawa wajen inganta shugabanci da tsara manufofi.
Waiya ya sake tabbatar da aniyar gwamnati na rungumar kowa a tafiyar da mulki, yana mai cewa ƙungiyoyin fararen hula abokan hulɗa ne masu muhimmanci wajen samar da ci gaba mai ɗorewa a Kano.
Ya bayyana ƙungiyoyin a matsayin ginshiƙai a harkokin raya kasa, tare da nuna buƙatar zurfafa haɗin kai, buɗe hanyoyin sadarwa da kuma ƙarfafa alaƙa tsakanin hukumomin gwamnati da masu zaman kansu.
Mahallarta taron sun bayyana zaman a matsayin mai ma’ana da hangen nesa, inda aka tattauna kan muhimman manufofi da dabarun da za su taimaka wajen bunƙasa jihar.
An kammala taron da sabunta alƙawarin ci gaba da aiki tare tsakanin gwamnati da ƙungiyoyin fararen hula domin inganta gaskiya, riƙon amana da kuma ayyukan ci gaba a Jihar Kano.



