Siyasa

Taron Karɓar Gwamna Abba zuwa APC: Nazari Kan Tsari, Tasiri da Shirin 2027

Taron bikin karɓar Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, zuwa APC da aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha Stadium, tare da halartar Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, ya haifar da muhawara kan yadda aka tsara taron da kuma tasirin sa ga zaɓen 2027.

 

Masu sharhi sun bayyana cewa taron ya zama wani ma’auni da ke nuna wanda ya fi shiri tsakanin Gwamna da manyan jagororin APC a Kano.

 

Duk da cewa Gwamnan ya yi iya ƙoƙarinsa, an nuna cewa wasu daga cikin waɗanda aka dora wa alhakin shirya taron daga ɓangaren gwamnati sun gaza wajen tattara magoya baya yadda ya kamata.

 

An lura cewa mafi yawan kayan kamfen da aka gani – riguna da huluna – sun fi ɗauke da sunayen jiga-jigan APC, maimakon alamomin magoya bayan Gwamnan.

 

Haka kuma, daga filin jirgin saman Malam Aminu Kano International Airport zuwa filin taron, an fi ganin tasirin manyan shugabannin jam’iyyar.

 

Taron ya kuma janyo tambayoyi kan rawar da shugabannin ƙananan hukumomi, kwamishinoni, ‘yan majalisa da mashawartan Gwamna suka taka, domin ba a ga fitowarsu yadda ake tsammani ba.

 

Masu nazari na ganin wannan na nuna buƙatar sake duba tsarin wayar da kai da haɗa jama’a daga matakin tushe.

A gefe guda kuma, taron ya fito da tasiri da ƙarfi na wasu jiga-jigan APC da suka haɗa da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai Barau I. Jibrin, Murtala Sule Garo, Abubakar Kabir Bichi, Baffa Babba Dan Agundi, da Alhassan Ado Doguwa.

 

An bayyana cewa jajircewarsu ta tabbatar da cewa APC na da tsari da ƙarfi a Kano.

 

Har ila yau, wasu sun danganta nasarar taron da saƙon siyasa da aka aikawa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da kuma tsohon Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, cewa jam’iyyar na nan daram a jihar.

Masu sharhi sun ba da shawarar cewa Gwamna ya yi duban tsanaki kan shugabancin ƙananan hukumomi 44 na jihar, domin ƙarfafa tsarin shirya gangami da haɗa jama’a. Sun kuma jaddada cewa haɗin kai da aiki tare da jiga-jigan APC zai zama muhimmin ginshiƙi wajen fuskantar zaɓen 2027.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button