Ana Zargin ’Yan Lakurawa Sun Kashe Mutum 30, Sun Lalata Ƙauyuka Bakwai a Kebbi

Wasu ’yan bindiga da ake zargin ’yan ƙungiyar Lakurawa ne sun kashe akalla mutum 30 tare da lalata ƙauyuka bakwai a hare-haren da suka kai a yankin arewa maso yammacin Jihar Kebbi.
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, Bashir Usman, ya shaida wa Agence France-Presse (AFP) cewa maharan sun kai farmakin ne a yankin Bui na ƙaramar hukumar Arewa da misalin ƙarfe 1:15 na rana a ranar Laraba.
Rahotanni sun nuna cewa adadin waɗanda suka mutu ya haura 30, musamman idan aka haɗa da mutanen da suka fito daga ƙauyukan Mamunu da
Awasaka da Tungan Tsoho da Makangara da Kanzo da Gorun Naidal da Dan Mai Ago domin kare kansu daga harin.
Wani mazaunin ƙauyen Kanzo ya bayyana cewa sun ji ƙarar harbe-harbe suna cikin gidajensu, lamarin da ya tilasta mutane guduwa neman mafaka, inda harsasai suka samu wasu daga cikinsu.
’Yan sanda sun kuma tabbatar da cewa maharan sun kwashe shanu da dama yayin farmakin.
Bayan harin, an tura jami’an tsaro da sojoji tare da ’yan sa-kai zuwa yankin domin daƙile lamarin da kuma ƙoƙarin dawo da zaman lafiya.




