Labarai

’Yan Sandan Yobe Sun Kama Mutane Hudu Kan Zargin Garkuwa da Mutum a Potiskum

Rundunar ’Yan Sandan reshen Jihar Yobe ta kama wasu mutane hudu da ake zargi da garkuwa da wani mutum bayan sun bayyana kansu a matsayin jami’an tsaro.

Jami’in Hulda da Jama’a na rundunar a jihar, SP Dungus Abdulkarim, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata 17 ga Fabrairu 2026.

 

A cewar sanarwar, lamarin ya faru ne a ranar 16 ga Fabrairu 2026 da misalin karfe 10:30 na dare, lokacin da jami’an ’yan sanda na ofishin Potiskum suka tare wata mota kirar Toyota Prado, inda suka samu nasarar ceto Abdulhamid Garba mai shekaru 35, dan asalin Damaturu.

 

Binciken farko ya nuna cewa wadanda ake zargin sun yaudare shi ne ta hanyar karyar su jami’an tsarone

 

Rundunar ta ce an kama Mohammed Usman, Kabiru Ibrahim Umar, Idriss Abdullahi Zakaria da Matthew Obata, tare da kwato motar Toyota Prado da aka yi amfani da ita wajen aikata laifin.

 

Ta kara da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike domin gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu domin su fuskanci hukunci bisa laifin da ake zarginsu da aikatawa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button