Kano: An Rufe Gidajen Gala da Harkokin DJ Har Zuwa Karshen Azumi

Sanarwar rufe wuraren ta fito ne ta bakin Jami’in Hulda da Jama’a na hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman, cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.
A cewar sanarwar, daga ranar Laraba 18 ga Fabrairu 2026 da karfe 10:00 na dare, dukkan cibiyoyin nishadi da suka hada da dakunan taro da aka fi sani da gidan gala, da kuma masu sana’ar DJ, za su kasance a rufe har zuwa kammala azumin watan Ramadan.
Hukumar ta bayyana cewa an dauki wannan mataki ne domin bai wa al’umma damar gudanar da azumi da sauran ibadu cikin natsuwa, kwanciyar hankali da kiyaye alfarmar watan mai alfarma.
Ta kuma kara da cewa za a sanar da ranar sake bude wuraren bayan kammala azumi, musamman yayin bukukuwan Sallah.
A karshe, hukumar ta bukaci masu ruwa da tsaki su ba da cikakken hadin kai tare da bin umarnin bisa dokar da ta kafa ta, tare da yin addu’ar Allah Ya sa a gudanar da Ramadan lafiya




