Labarai

Babbar Kotun Tarayya a Kano Ta Yanke Wa Ma’aikaciyar Banki hukuncin Daurin Shekaru 5 a Gidan yari

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Kano ta tabbatar da laifi tare da yanke wa wata mata mai suna Janet Theophilus Danjuma hukuncin daurin shekaru biyar a gidan yari, bisa laifin damfarar kudi har naira miliyan 22 da dubu 350.

 

An gurfanar da wadda ake tuhuma a ranar 16 ga Fabrairu a gaban Mai Shari’a S. M. Shuaibu, bisa tuhume-tuhume da ya shafi karɓar kudi ta hanyar yaudara.

 

A cewar tuhumar, Janet Danjuma, wadda ma’aikaciya ce a Taj Bank Limited, reshen Nai’bawa a Kano, ta karɓi kudin daga Wade Bamaiyi a watan Oktoba, 2024, inda ta yi ikirarin cewa za a saka kudin cikin shirin CASA na bankin.

Sai dai bincike ya nuna cewa ba a saka kudin ba

Laifin ya sabawa sashe na 1(1)(b) na dokar da ta haramta damfara, wanda hukuncinsa ke karkashin sashe na 1(3) na dokar.

Bayan karanta mata tuhumar, ta amsa laifinta.

Lauyan gwamnati mai gabatar da kara, Sadiq Huseini, ya bayyana yadda wadda ake tuhuma ta yaudari wanda ta karɓi kudin daga gare shi ta hanyar amfani da sunan wani sahihin shirin banki domin samun amincewa.

 

Mai Shari’a S. M. Shuaibu ya same ta da laifi tare da yanke mata hukuncin daurin shekaru biyar a gidan yari ba tare da zabin biyan tara ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button