Labarai

Rundunar ’yan sandan Bauchi ta ceto wani matashi bayan shafe kusan shekara 17 a ɗaure da sarka a cikin gida

Rahotanni sun nuna cewa ana zargin mahaifinsa, Mohammed Lawan, da garkame shi tare da ɗaure shi da sarka tsawon wannan lokaci.

Lamarin ya fito fili ne bayan wani mutum ya kai ƙorafi ga jami’an tsaro, wanda hakan ya sa rundunar ta ɗauki matakin gaggawa.

 

’Yan sanda sun kai samame a ƙauyen Shadawanka da ke jihar Bauchi, inda suka tarar da Muhammad Lawan cikin mawuyacin hali.

 

Daga nan ne jami’an suka kunce shi tare da fitar da shi daga inda aka tsare shi.

 

A cewar rundunar, an garzaya da shi asibiti domin a ba shi kulawar lafiya da ta dace.

 

Haka kuma, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Bauchi, Sani-Omolori Aliyu, ya bayar da umarnin kama mahaifin nasa domin gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

 

Rundunar ta tabbatar da cewa za ta bi diddigin lamarin har sai an gano gaskiya tare da tabbatar da adalci.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button