Labarai

Gwamnatin Tarayya da Gwamnonin APC Sun Tallafa wa ‘Yan Kasuwar Singa da Biliyan 8

Gwamnatin Tarayya da ƙungiyar gwamnonin APC sun bayar da tallafi ga ‘yan kasuwar da gobara ta shafa a Kasuwar Singa.

Jaridar Rimin Gado Updates ta rawaito cewa Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ne ya bayar da tallafin naira biliyan 5 a madadin Gwamnatin Tarayya, yayin ziyarar jajantawa da ya kai wa ‘yan kasuwar a ranar Litinin, 16 ga Fabrairu, 2026.

 

Haka kuma, ƙungiyar gwamnonin jam’iyyar APC ta sanar da bayar da ƙarin tallafin naira biliyan 3 domin taimaka wa waɗanda gobarar ta shafa.

Rahotanni sun bayyana cewa gobarar da ta tashi a ranar Asabar ta yi sanadiyyar asarar rayuka da dukiya mai tarin yawa, lamarin da ya jefa ‘yan kasuwa cikin mawuyacin hali.

An bayyana cewa tallafin da aka bayar na da nufin rage radadin asarar da aka yi, tare da farfaɗo da harkokin kasuwanci a kasuwar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button