Labarai

Gwamnatin Sokoto Ta Ware Naira Biliyan 1 Domin Ciyarwa a Ramadan 2026

Gwamnatin Jihar Sokoto ta amince da ware naira biliyan 1 domin aiwatar da shirin ciyarwa na watan Ramadan na shekarar 2026, inda ake sa ran rabon abinci ga mutum 34,000 a kowace rana a faɗin jihar.

Gwamnan jihar, Ahmed Aliyu, ne ya ƙaddamar da shirin a birnin Sokoto, yana mai bayyana cewa an ƙara yawan cibiyoyin ciyarwa daga 155 zuwa 170 domin biyan buƙatar jama’a.

A cewarsa, kowace cibiya za ta rika ciyar da kimanin mutum 200 a lokaci guda, domin tabbatar da cewa mabukata sun samu sauƙin samun abinci a watan azumi.

Jaridar The Punch ta ambato gwamnan yana cewa shirin ciyarwar, wanda aka fara tun a zamanin tsohon gwamnan jihar, Aliyu Wamakko, ya ci gaba da taimaka wa dubban al’umma wajen rage radadin talauci da tallafa musu a lokacin Ramadan.

Gwamnan ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da bullo da shirye-shiryen jin ƙai domin tallafa wa marasa ƙarfi a jihar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button