Shugabancin Kasuwar Singa Ya Musanta Yaduwar Gobara Zuwa Sabon Gari

Shugabancin Kasuwar Singa ya karyata rahotannin da ke cewa gobarar da ta tashi a kasuwar ta tsallaka zuwa Kasuwar Sabon Gari.
Shugaban Ƙungiyar ’Yan Kasuwar Singa, Barista Junaidu Muhammad Zakari, ne ya tabbatar wa APN Hausa cewa labarin ba shi da tushe balle makama.
Ya ce duk da cewa gobara na ci gaba da tashi a Kasuwar Singa, ba ta tsallaka zuwa Kasuwar Sabon Gari ba.
A cewarsa, ana ci gaba da kokarin shawo kan lamarin a bangaren Singa, tare da tabbatar da cewa ba a samu yaduwar gobarar zuwa sauran kasuwanni ba.
Hakazalika, wani daga cikin ’yan kasuwar Sabon Gari ya tabbatar da cewa gobarar ba ta kai bangarensu ba.
Sai dai ya bayyana cewa wasu daga cikin ’yan kasuwar sun koma shagunan su domin yin shirin ko-ta-kwana, domin dakile duk wata yiwuwar hadari.
Rahotanni na nuni da cewa jami’an da abin ya shafa na ci gaba da bibiyar lamarin domin tabbatar da tsaro da kare dukiyoyin ’yan kasuwa.




