Shugaba Ahmed Tinubu Ya Umarci da ayi Bincike Kan Gobarar Kasuwar Singer

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin gudanar da ƙwaƙƙwaran bincike kan musabbabin gobarar da ta tashi a Kasuwar Singer da ke Jihar Kano.
Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Mai ba Shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Lahadi, 15 ga Fabrairu, 2026.
Sanarwar ta bayyana cewa gobarar ta haddasa asarar dukiya mai yawa, lamarin da ya jefa ‘yan kasuwa cikin jimami da damuwa.
Haka kuma, Shugaban ƙasar ya tuntubi gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, domin jin halin da ake ciki tare da neman cikakken rahoto kan faruwar lamarin da matakan da ake dauka.
Rahotanni sun ce gobarar ta fara ne daga wani gidan gilas da ke cikin kasuwar a yammacin ranar Asabar, kafin ta bazu zuwa wasu shaguna da ke kusa, inda ta yi sanadiyyar barnar dukiya mai tarin yawa.
Shugaban ƙasar ya jajanta wa ‘yan kasuwar da abin ya shafa tare da jaddada aniyar gwamnatin tarayya na gano musabbabin gobarar da kuma daukar matakan da suka dace domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.




