Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Sauke Buba Galadima daga mukamin Shugaban Kano Poly

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sauke Injiniya Buba Galadima daga mukamin Shugaban Hukumar Gudanarwar Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kano.
Rahoton Arewa Updates ya bayyana cewa matakin na kunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labaran Gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Asabar 14 ga Fabrairu, 2026.
Sanarwar ta ce Gwamnan ya amince da nadin Aliyu Ibrahim Abdulkadir, Sarkin Gaya, a matsayin sabon Shugaban Hukumar Gudanarwar makarantar.
A cewar sanarwar, sauke Galadima ya biyo bayan sake fasalin tsarin gudanarwa da daidaita ayyuka domin dacewa da ajandar #KanoFirst ta gwamnatin jihar.
Gwamnan ya gode wa Injiniya Buba Galadima bisa gudunmawar da ya bayar a lokacin da yake rike da mukamin, tare da bukatar sabon shugaban ya yi amfani da kwarewarsa wajen bunkasa harkokin ilimi da inganta tsarin gudanarwa a makarantar.
Sauyin ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun muhawara a siyasance, musamman bayan rabuwar kai tsakanin gwamnatin Kano da tsohon jagoranta, Rabiu Musa Kwankwaso.




