Majalisar Wakilai Za Ta Yi Zaman Gaggawa Kan Jadawalin Zaɓen 2027

Majalisar Wakilan Najeriya ta sanar da cewa za ta gudanar da zaman gaggawa a ranar Talata 17 ga watan Fabrairu, 2026 domin nazari kan batutuwan da suka taso sakamakon fitar da jadawalin zaɓen 2027 da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta yi.
Sanarwar ta fito ne ta bakin mai magana da yawun majalisar, Hon. Akin Rotimi, wanda ya bayyana cewa an sanar da mambobin majalisar ne ta wata takarda ta cikin gida da ofishin shugaban majalisar ya fitar a yammacin ranar Juma’a.
Majalisar ta ce kiran zaman gaggawar na nuni da ƙudurin ta na duba duk wani lamari da ka iya shafar tsarin dimokuraɗiyyar ƙasa, tare da tabbatar da cewa an bi doka da ƙa’ida kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada.
A ranar Juma’a ne INEC ta sanar da cewa za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na ƴan majalisar tarayya a ranar 20 ga watan Fabrairu, 2027, yayin da za a gudanar da zaɓen gwamnoni da na ƴan majalisar jiha a ranar 6 ga watan Maris, 2027.
Sai dai sanarwar ta jawo muhawara a tsakanin wasu ƴan Najeriya, musamman al’ummar musulmi, waɗanda suka nuna damuwa kan cewa ranar zaɓen shugaban ƙasa ta faɗo ne a cikin watan Ramadan, lamarin da suka ce na iya shafar halartar masu kaɗa ƙuri’a.
Ana sa ran zaman majalisar zai mayar da hankali ne kan nazari da tattaunawa kan jadawalin zaɓen, tare da duba matakan da suka dace domin tabbatar da adalci da sauƙin gudanar da zaɓe ga kowa.



