Atiku Ya Bukaci INEC Ta Sake Duba Ranakun Zaɓen 2027

Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya yi kira ga Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da ta gaggauta sake nazari kan ranar da aka tsayar domin gudanar da babban zaɓen 2027, yana mai cewa lokacin ya yi karo da watan Ramadan.
A ranar Juma’a ne INEC ta sanar da cewa za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na ƴan majalisun tarayya a ranar 20 ga watan Fabrairu, 2027, yayin da za a gudanar da zaɓen gwamnoni da na ƴan majalisun jihohi a ranar 6 ga watan Maris, 2027.
Sai dai cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, Atiku ya ce ranar 20 ga Fabrairu ta faɗo a tsakiyar watan Ramadan, wanda ya bayyana a matsayin lokaci mai muhimmanci na azumi da ibada ga miliyoyin Musulmin Najeriya.
Ya ce sanya babban zaɓen ƙasa a irin wannan lokaci na ibada na iya nuna rashin la’akari da al’amuran zamantakewa da addini na ƙasar, yana mai jaddada cewa ya dace a yi la’akari da yadda Najeriya ta ƙunshi al’ummomi mabambanta kafin a yanke duk wata muhimmiyar shawara.
A nata ɓangaren, INEC ta bayyana cewa zaɓen ranakun ya yi ne bisa tanade-tanaden Kundin Tsarin Mulkin 1999, wanda ya tsara iyakokin lokacin gudanar da zaɓe.



