Labarai

Magoya Bayan Waiya Sun Nuna Bacin Rai Kan Naɗin Kwamitin Karɓar Gwamna Abba Zuwa APC

Magoya bayan Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kano, Ibrahim Abdullahi Waiya, sun ci gaba da nuna bacin ransu kan yadda aka naɗa shi memba kawai a Kwamitin Yaɗa Labaran Karɓar Gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa jam’iyyar APC.

 

Rahotanni sun nuna cewa rikicin ya fi bayyana a kafafen sada zumunta, musamman a shafin Facebook, inda magoya bayan Waiya ke wallafa saƙonni da sharhi suna bayyana rashin jin daɗinsu kan tsarin kwamitin.

A cewar su, ya kamata a bai wa Waiya shugabancin kwamitin duba da matsayinsa na Kwamishinan Yaɗa Labarai a gwamnatin Kano.

An dai naɗa tsohon Kwamishinan Yaɗa Labarai, Malam Muhammad Garba, a matsayin Shugaban Kwamitin, yayin da Daraktan Janar na Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Gidan Gwamnatin Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, aka naɗa a matsayin Sakataren kwamitin.

Wasu daga cikin magoya bayan jam’iyyar na kallon matakin a matsayin raini ko rashin la’akari da rawar da Waiya ke takawa, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin mabiya APC a jihar.

Tuni dai magoya bayan Kwamishinan suka fara kira ga shugabannin jam’iyyar da su sake duba tsarin kwamitin domin kauce wa rikici da rarrabuwar kai a cikin jam’iyyar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button