Labarai

Gwamnatin Kano Ta Jaddada Aniyarta Na Bunkasa Al’adu Don Samar Da Ayyukan Yi

Gwamnatin Jihar Kano ta sake jaddada kudirinta na ci gaba da bunkasa harkokin al’adu domin karfafa hadin kai da samar da ayyukan yi ga matasa a fadin jihar da ma kasa baki daya.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan yayin kaddamar da gasar tseren motoci da aka gudanar a matsayin wani bangare na bukukuwan Bikin Kamun Kifi na Argungu a Jihar Kebbi.

Gwamnan, wanda Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya wakilta, ya ce bukukuwan al’adu na taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa tattalin arziki, karfafa zamantakewa da kuma bai wa matasa damar nuna hazaka da kirkire-kirkire.

Ya kara da cewa gwamnatin Kano za ta ci gaba da tallafawa shirye-shiryen da ke kare al’adu tare da samar da sabbin damammaki ga matasa domin su dogara da kansu.

A cewarsa, gwamnatin ta kuma saukaka halartar tawagar da ta shirya gasar tseren motocin, wacce ta kasance daya daga cikin manyan abubuwan jan hankali a bikin na bana.

Da yake nasa jawabin, Shugaban Kwamitin Shirya Bikin kuma tsohon Daraktan Hulda da Hular Gargajiya da Ka’idojin Motoci a Jihar Kebbi, Ibrahim Sulaiman, ya bayyana Bikin Kamun Kifi na Argungu a matsayin daya daga cikin manyan bukukuwan al’adu na duniya.

Ya ce bikin na jawo mahalarta da masu yawon bude ido daga sassa daban-daban na duniya, tare da zama wata muhimmiyar kafa ta musayar al’adu, bunkasa yawon bude ido da kuma karfafa tattalin arziki ga al’ummar da ke karbar bakunci da ma kasa baki daya.

Sulaiman ya yaba da hadin gwiwar da ke tsakanin Jihohin Kano da Kebbi wajen tabbatar da nasarar bikin.

 

Taron ya samu halartar Kwamishinar Al’adu da Yawon Bude Ido ta Jihar Kano, Aisha Lawal Sagi, da sauran manyan baki daga sassa daban-daban na kasa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button