Gwamnan Sakkwato Ya Amince da Biyan Albashi da Wuri Domin Ramadan

Gwamnan Jihar Sakkwato, Ahmed Aliyu, ya amince da biyan albashi da wuri ga ma’aikatan jihar domin sauƙaƙa musu halin rayuwa yayin da ake shirin fara azumin watan Ramadan.
Sanarwar da Daraktan Yaɗa Labaran Gwamnan, Abubakar Bawa, ya fitar ta bayyana cewa matakin na daga cikin ƙoƙarin gwamnati na tallafa wa ma’aikata tare da rage musu matsin tattalin arziƙi a wannan lokaci na ibada.
A cewar sanarwar, biyan albashin da wuri zai bai wa ma’aikata damar shiryawa azumi cikin walwala da kwanciyar hankali.
Matakin ya shafi ma’aikatan Gwamnatin Jiha, na Ƙananan Hukumomi, ma’aikatan Hukumar Ilimi ta Ƙananan Hukumomi (LGEA), da kuma tsofaffin ma’aikata masu karɓar fansho a faɗin jihar.
Gwamnatin ta jaddada kudirinta na ci gaba da ɗaukar matakan da za su inganta jin daɗin ma’aikata da al’ummar jihar baki ɗaya.




