‘Yan Majalisar Amurka Sun Gabatar da Ƙuduri Kan Zargin Cin Zarafin Kiristoci a Najeriya

Wasu ‘yan Majalisar Wakilan Amurka sun gabatar da wani ƙuduri a zauren majalisar, wanda ya ƙunshi rahoton wani kwamitin bincike kan zargin cin zarafin Kiristoci da musguna musu a Najeriya.
Ƙudurin, wanda wasu ‘yan majalisa na jam’iyyar Republican suka gabatar, ya kuma ƙunshi shawarwari kan matakan da gwamnatin Amurka za ta iya ɗauka domin magance matsalar.
A cikin ƙudurin, ‘yan majalisar sun buƙaci Sakataren Harkokin Wajen Amurka da ya ayyana wasu ƙungiyoyin ‘yan bindiga a matsayin ƙungiyoyin ta’addanci, tare da la’akari da sanya takunkumi kan wasu ‘yan Najeriya da ake zargi da hannu a take haƙƙin Kiristoci.
Haka kuma, ƙudurin na neman a ɗauki wasu matakai da suka haɗa da hana shigar wasu mutane cikin Amurka, idan aka tabbatar da hannu a laifukan da ake zargi.



