Tinubu Ya Naɗa Ambasada Ismail Abba Yusuf a Matsayin Shugaban NAHCON

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Fadar Shugaban Ƙasa ta fitar, mai ɗauke da sa hannun mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga.
Sanarwar ta ce naɗin na jiran amincewar Majalisar Dattawa, kamar yadda sashe na 3(2) na dokar NAHCON ta shekarar 2006 ta tanada.
Shugaba Tinubu ya kuma aike da wasiƙa ga Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, inda ya buƙaci a gaggauta tantancewa da amincewa da naɗin Ambasada Yusuf, domin ya maye gurbin Farfesa Abdullahi Usman, wanda ya yi murabus a wannan mako bayan shafe kusan watanni 14 a kan muƙamin.
Ambasada Ismail Abba Yusuf ƙwararren jami’in diflomasiyya ne, wanda ya taɓa zama Jakadan Najeriya a ƙasar Türkiye daga shekarar 2021 zuwa 2024.
Ana sa ran idan Majalisar Dattawa ta amince da naɗin, sabon shugaban zai jagoranci hukumar NAHCON wajen shirye-shiryen aikin Hajjin bana da sauran ayyukan da suka shafi kula da mahajjatan Najeriya.




