Labarai

Sarkin Kano Ya Buƙaci ‘Yan Kasuwa Su Sauƙaƙawa Al’umma Yayin da al’ummar Musulmi ke shirye-shiryen fara azumin watan Ramadan

Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya yi kira ga ‘yan kasuwa da su sauƙaƙawa jama’a farashin kayayyaki, domin rage musu radadin tsadar rayuwa a wannan lokaci na ibada.

Sarkin ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ƙaddamar da Ƙungiyar Daliban Masarautar Kano, a wani taro da aka gudanar a Fadar Sarkin Kano da ke Nassarawa a Birnin Kano.

 

Alhaji Aminu Ado Bayero ya ce a irin wannan lokaci da Musulmi ke shirin shiga watan Ramadan, ya dace ‘yan kasuwa a ko’ina su nuna tausayi tare da rage farashin kayayyakin masarufi, domin bai wa jama’a damar siyan abin da za su buƙata a watan azumi da ma bayan sa.

 

Sarkin ya kuma buƙaci al’umma da su zage damtse wajen ibada, tare da kasancewa cikin tsarkakakkiyar zuciya da yawaita addu’o’i domin samun zaman lafiya, bunƙasar tattalin arziki da ci gaban masana’antu.

 

Haka zalika, ya yi kira ga malamai da su ci gaba da fadakar da al’umma kan kaucewa munanan halaye, tare da ƙarfafa zaman lafiya da kyautatawa juna.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button