Labarai

Isma’ila Abba Tangalashi Ya Ajiye Aiki da Hikima Radio

Fitaccen ɗan jarida a ɓangaren wasanni, Isma’ila Abba Tangalashi, ya ajiye aikinsa da Hikima Radio Kano, lamarin da ke ƙara nuna sauye-sauyen da ake samu a tashar a baya-bayan nan.

Rahotanni sun nuna cewa ficewar Tangalashi ta biyo bayan wasu sauye-sauye a gidan rediyon, kwanaki kaɗan bayan da Shugaban tashar, Malam Abubakar Isah Dandago, da kuma Shugaban Sashen Siyasa, Malam Aliyu Sufyan Alhassan, suka sanar da barin aikinsu.

Tangalashi ya fara aikin jarida ne a Gidan Rediyon Jihar Kano, kafin daga bisani ya yi aiki da Aminci Radio Kano da Vision FM Kano.

Haka kuma ya yi aiki da Tambarin Hausa TV da Arewa24, kafin daga ƙarshe ya koma Hikima Radio Kano.

 

Ya yi fice wajen gabatar da labaran wasanni da kuma sharhin wasanni (commentary) a harshen Hausa, inda ya samu karɓuwa a tsakanin masu sauraro da masu kallo.

Baya ga aikin jarida, Tangalashi na riƙe da muƙamin Mataimakin Kakakin Hukumar Kwallon Ƙafa ta Kano Pillars, inda ya samu yabo sakamakon ƙwarewarsa da jajircewarsa a fagen wasanni.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button