Labarai

An Tsinci Gawar Wani Matashi da Ake Zargin Ya Rataye Kansa a Gyadi-Gyadi

Lamarin ya jawo hankalin mazauna yankin ne da misalin lokacin da jama’a ke fitowa domin sallar Asubah, inda aka hangi gawarsa a rataye.

 

Wasu shaidun gani da ido sun shaida wa wakilinmu cewa sun fara lura da al’amarin ne da safe, lamarin da ya haddasa taruwar jama’a kafin a sanar da jami’an tsaro.

 

Kwamandan ƙungiyar sa-kai ta vigilante a Gyadi-Gyadi, Abdulrahman Muhammad (Babayo), ya ce da ya samu labarin faruwar lamarin, nan take ya kira jami’an ‘yan sanda domin su zo su ɗauki matakin da ya dace.

 

A nasa ɓangaren, Dagacin unguwar Gyadi-Gyadi, Nura Aliyu Abbas, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Sai dai ya bayyana cewa marigayin na fuskantar wasu matsaloli na rashin kwanciyar hankali, yana mai zargin cewa matsalar ta samo asali ne bayan an ce ya taɓa samun wasu kuɗaɗe ta hanyar yin caca (Chacha), waɗanda daga bisani aka kwace ko aka janye su.

Dagacin ya yi kira ga iyaye da su ƙara sanya ido kan ‘ya’yansu, tare da kula da irin abokan hulɗa da mu’amalolin da suke yi, domin kauce wa faruwar irin wannan lamari a nan gaba.

Jami’an tsaro sun ɗauki gawar domin ci gaba da bincike kan musabbabin mutuwar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button