Tashar Rediyo da Masarautar Madobi Sun Dauki Nauyin Mayar da Yara 680 Makaranta

A wani gagarumin yunkuri na bunkasa ilimi, tashar rediyo ta Himma da ke Kano, tare da hadin gwiwar Masarautar Madobi, sun kaddamar da wani shiri na musamman na mayar da yara makaranta a Karamar Hukumar Madobi.
Tashar ta Himma Radio ce ta fara daukar nauyin mayar da yara 80 da ba sa zuwa makaranta, a wani bangare na shirinta na hidimtawa al’umma.
A nasa jawabin, shugaban tashar, Alhaji Isma’il Yusuf Makwarari, ya bayyana cewa wannan shiri an assasa shi ne domin bayar da gudunmawa wajen ci gaban al’umma.
Da yake nuna goyon bayansa, Hakimin Madobi, Alhaji Sale Musa Sale (Kwankwaso), ya yi alkawarin daukar nauyin mayar da wasu yara 600 makaranta.
Ya ce a madadin kansa da sauran masu rike da sarautun gargajiya, za su dauki nauyin yara 50 a kowace mazaba daga cikin mazabu 12 na karamar hukumar.
A nasa bangaren, Shugaban Karamar Hukumar Madobi, Sulaiman Dan Azumi, wanda kansilan mazabar Kafin Agur, Hon. Tijjani Rabi’u Kafi ya wakilta, ya tabbatar da cewa karamar hukumar za ta bayar da tata gudunmawar domin ci gaban ilimi a yankin.
Biyo bayan shawarar da shugaban tashar Himma Radio ya bayar, Hakimin Madobi ya amince da kafa wani asusu na musamman domin tallafawa ilimi, wanda za a kira “Madobi Education Trust Funds”. Ya kuma bayar da wa’adin watanni uku domin kaddamar da asusun.
Sakataren Ilimi na Karamar Hukumar, Lawan Sani Gora, ya yi kira ga iyayen yaran da aka dauki nauyi da su tabbatar da cewa ‘ya’yansu suna zuwa makarantar kamar yadda ya kamata domin ganin an cimma nasarar shirin.




