Tinubu: Za Mu Yi Galaba kan Ta’addanci da ’Yan Bindiga a Najeriya

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta yi galaba kan matsalolin ta’addanci da ’yan bindiga a Najeriya, yana mai bayyana rashin tsaro a matsayin ƙalubalen da ƙasar ba ta fuskanta da irinsa ba a baya.
Shugaban ƙasar ya bayyana hakan ne yayin buɗe taron Majalisar Tattalin Arziki ta Ƙasa (NEC) da aka gudanar a fadar gwamnati da ke Abuja.
A cewarsa, gwamnati na ɗaukar matakai masu ƙarfi domin ƙarfafa jami’an tsaro da nufin dawo da zaman lafiya a faɗin ƙasar.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Mai Magana da Yawun Fadar Shugaban Ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar, inda ya ce rashin tsaro na kawo cikas ga bunƙasar tattalin arziki, don haka ya zama wajibi kowa ya bada gudummawa wajen shawo kan matsalar.
Shugaba Tinubu ya yabawa gwamnonin jihohin Borno, Katsina da Kaduna bisa ƙoƙarin da suke yi wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma a jihohinsu.
A ɓangaren tattalin arziki, shugaban ƙasar ya bayyana cewa sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatinsa ta aiwatar sun fara haifar da sakamako mai kyau, tare da ƙara kwarin gwiwa ga manufofin kuɗi na ƙasar.
Haka kuma, ya yabawa Babban Bankin Najeriya (CBN) kan rawar da yake takawa.
Tinubu ya ƙara da cewa jihohi da ƙananan hukumomi yanzu suna samun ƙarin kuɗaɗen shiga daga tarayya, lamarin da ke ba su damar biyan albashi da aiwatar da ayyukan more rayuwa ga al’ummarsu.
Har ila yau, shugaban ƙasar ya bayyana cewa sabon Shirin Ci Gaban Ƙasa na “Renewed Hope” na shekarun 2026 zuwa 2030 zai mayar da hankali ne kan bunƙasa tattalin arziki, inganta rayuwar al’umma, da samar da ci gaba mai ɗorewa a Najeriya.



