Majalisar Kano ta bukaci gwamnati ta Gina Babban Asibiti a Tamburawa

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi karatu na biyu kan ƙudirin dokar kafa Hukumar Kula da Ma’aikatan Ƙananan Hukumomi ta shekarar 2025, tare da karanto ƙudirin dokar Hukumar Ayyuka ta Majalisar Dokokin Jihar Kano ta shekarar 2026.
Zaman majalisar ya kuma shaida karɓar wani ƙudurin haɗin gwiwa da ’yan majalisun Bunkure da Kibiya, Kura da Garin Malam, da kuma Rano suka gabatar, ƙarƙashin jagorancin ɗan majalisa mai wakiltar Rano, Ibrahim Muhammad Rano.
Bugu da ƙari, majalisar ta bukaci gwamnatin Jihar Kano da ta ɗauki matakin gaggawa wajen gina babban asibiti a garin Tamburawa, da ke cikin ƙaramar hukumar Dawakin Kudu, domin sauƙaƙa wa al’ummar yankin samun ingantacciyar kulawar lafiya.
Majalisar ta jaddada cewa samar da irin wannan cibiyar lafiya zai taimaka matuƙa wajen rage wahalhalun da mazauna yankin ke fuskanta, musamman wajen tafiya nesa domin neman magani, tare da inganta lafiyar al’umma baki ɗaya.



