Hukumar Road Safety Ta Fayyaɗa Gaskiya kan Mummunan Hatsarin Motar da ya afku a Kano

Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC) ta yi ƙarin bayani kan wani mummunan hatsarin mota da ya auku a Jihar Kano, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane da jikkatar wasu da dama.
Hatsarin ya faru ne sakamakon adunguren wata babbar mota a kan hanyar zuwa Gujungu, a Jihar Jigawa.
Lamarin ya rutsa da mutane da dama, inda wasu suka rasa rayukansu yayin da wasu kuma suka jikkata.
Da farko, gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa hatsarin ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 30. Sai dai bayan kammala binciken da ta gudanar, Hukumar Road Safety ta ce adadin mutanen da suka mutu ya tsaya ne a bakwai.
Jami’in Hulɗa da Jama’a da Wayar da Kai na Hukumar FRSC reshen Jihar Kano, CRC Abdullahi Labaran, ya shaida cewa bayanan da aka tattara sun nuna cewa gudun wuce kima da tuƙin ganganci su ne manyan abubuwan da suka haddasa hatsarin.
Ya ƙara da cewa, sakamakon yawan mutanen da suka jikkata, an raba su zuwa asibitoci huɗu daban-daban domin samun kulawar gaggawa.
Rahotanni na nuna cewa ana yawan fuskantar haɗurran mota a manyan titunan Najeriya, lamarin da ake danganta shi da rashin kyawun hanyoyi, tuƙin ganganci, da gudun da ya wuce kima da direbobi ke yi.



