Labarai

NDLEA Ta Kama Ɗan Kasuwa Da Hodar Iblis Kullu 95 A Filin Jirgin Sama Na Kano

Rahotanni sun nuna cewa jami’an NDLEA sun cafke Izueke ne yayin binciken tsaro kafin tashinsa, inda aka gano kullu 95 na hodar iblis mai nauyi da aka ɓoye a kayansa, wanda jimillar nauyinsu ya kai kilogiram 1.589.

Binciken farko da hukumar ta gudanar ya nuna cewa wanda ake zargin ya yi niyyar safarar miyagun ƙwayoyin ne domin tara kuɗin da zai kammala ginin wani gida da yake yi a kauyensu.

Hukumar NDLEA ta bayyana cewa an kama wanda ake zargin tare da dukkan kayan laifin, kuma an fara gudanar da cikakken bincike domin gano masu hannu a wannan safara da kuma gurfanar da shi gaban kuliya bisa tanadin doka.

 

NDLEA ta kuma sake jaddada aniyarta ta ci gaba da ƙarfafa matakan tsaro a dukkan filayen jiragen sama da iyakokin ƙasar nan, domin dakile fataucin miyagun ƙwayoyi da ke barazana ga lafiyar al’umma da tsaron ƙasa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button