Majalisar Dokokin Kano Ta Musanta Shirin Tsige Mataimakin Gwamna

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta musanta rahotannin da ke yawo a wasu kafafen yaɗa labarai da ke ikirarin cewa majalisar na shirin tsige Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo.
Mai magana da yawun Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano, Kamaluddeen Sani Shawai, ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai a Kano.
Ya jaddada cewa babu wani shiri ko yunƙuri a majalisar da ya shafi tsige mataimakin gwamnan, yana mai bayyana irin waɗannan rahotanni a matsayin marasa tushe balle makama.
Shawai ya ƙara da cewa Majalisar Dokokin Jihar Kano na ci gaba da gudanar da ayyukanta bisa tanadin doka da kundin tsarin mulkin ƙasa, ba tare da kaucewa ka’idojin da suka tanada ba.
Ya kuma yi kira ga al’umma da su yi watsi da duk wani labari da ba a tabbatar da sahihancinsa ba, tare da dogaro da sahihan bayanai daga majalisar ko hukumomin da abin ya shafa.




