Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sabbin Gidajen Sojoji a Jihar Sokoto

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da sabbin gidajen sojoji da aka gyara a Giginya Cantonment da ke Jihar Sokoto, domin inganta walwalar kananan sojoji daga matsayin Kofur zuwa ƙasa.
Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ne ya ƙaddamar da gidajen a madadin Gwamnatin Tarayya, inda ya bayyana cewa matakin na daga cikin manyan ƙoƙarin gwamnati na inganta rayuwar jami’an tsaro, musamman waɗanda ke aiki a yankin Arewa maso Yamma da ke fuskantar ƙalubalen tsaro.
Ministan ya jaddada cewa samar da ingantattun gidaje ga sojoji ba wani gata ba ne, sai dai hakki ne da ya rataya a wuyan gwamnati, la’akari da irin sadaukarwar da sojoji ke yi wajen kare ƙasar nan.
Ya ƙara da cewa kula da walwalar sojoji na taka muhimmiyar rawa wajen ƙarfafa ɗa’a, ƙara ƙwazo da kuma tabbatar da nasarar ayyukan tsaro.
A nasa jawabin, Kwamandan Runduna ta 8, Birgediya Janar Abdumalik Muhammed, ya bayyana aikin a matsayin wanda ya zo a kan lokaci, yana mai cewa gyaran gidajen zai ƙara wa sojoji ƙwarin gwiwa da kuzari wajen ci gaba da yaƙi da ’yan bindiga da sauran barazanar tsaro a yankin.
Ya kuma yaba wa Gwamnatin Tarayya da Ma’aikatar Tsaro bisa kulawar da suke bai wa walwalar jami’an soji, yana mai bayyana cewa hakan na nuna jajircewar gwamnati wajen tallafa wa rundunar soji a fagen tsaro.




