Gwamnatin Sokoto Ta Musanta Zargin Bai Wa Ƴar TikTok Kyautar Mota

Gwamnatin Jihar Sokoto ƙarƙashin jagorancin Gwamna Ahmed Aliyu ta musanta rahotannin da ke yawo a shafukan sada zumunta da ke iƙirarin cewa gwamnan na da hannu wajen bai wa wata shahararriyar ƴar TikTok kyautar mota.
Musanta zargin na zuwa ne cikin wata sanarwa da Daraktan Harkokin Yaɗa Labarai na gwamnan jihar, Abubakar Bawa, ya fitar, inda ya bayyana cewa ofishin gwamnan ya tsame kansa gaba ɗaya daga batun bayar da kyautar, yana mai jaddada cewa babu wata alaƙa, ta kowace fuska, tsakanin gwamnan da lamarin.
Sanarwar ta ce rahoton ba shi da tushe, tare da bayyana shi a matsayin jita-jita da ba su dace ba.
Lamarin ya fara ne a ƙarshen makon da ya gabata, bayan wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta, wanda ke nuna wasu maza biyu suna miƙa kyautar mota ga wata sananniyar ƴar TikTok a birnin Sokoto, abin da ya janyo muhawara a tsakanin jama’a.
A cikin bidiyon, mutanen sun yi iƙirarin cewa sun ba ta motar ne a matsayin kyautatawa, sakamakon “soyayyar” da suke cewa tana nunawa ga gwamnan jihar.
Sai dai batun ya jawo suka daga wasu masu amfani da kafafen sada zumunta, inda wasu ke zargin cewa an yi amfani da kuɗaɗen gwamnati wajen siyan motar, zargin da gwamnatin jihar ta musanta gaba ɗaya.



