Rikici Ya ɓarke a Taron Masu Ruwa da Tsaki na APC a Dawakin-Tofa/Tofa/Rimingado

Rikici ya ɓarke a taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC da aka gudanar a mazaɓar Dawakin-Tofa/Tofa/Rimingado a Jihar lamarin da ya kai ga tarwatsa taron tare da jikkata wasu mahalarta.
Rahotanni sun nuna cewa rikicin ya samo asali ne bayan da Hajiya Hasiya Aminu, shugabar mata ta jam’iyyar NNPP a Dawakin-Tofa wadda ta koma APC, ta ƙalubalanci ɗan majalisar tarayya mai wakiltar yankin, Tijjani Abdulkadir Jobe, kan abin da ta kira gazawarsa wajen kula da ‘yan jam’iyya.
Wata jaridar yanar gizo, Arewa Updates, ta rawaito cewa Hajiya Hasiya ta yi kira ga ɗan majalisar da ya yi koyi da Shugaban Karamar Hukumar Dawakin-Tofa, Anas Mukhtar Bello DanMaliki, da kuma Engr. Abba Ganduje, kalaman da suka fusata Tijjani Jobe.
Rahotanni sun ƙara da cewa, yayin da Hajiya Hasiya ke tsaka da jawabi, ɗan majalisar ya yi yunƙurin miƙewa domin ba da amsa, amma aka hana shi tare da kwace lasifika, lamarin da ya ƙara ruruta wutar rikicin.
A sakamakon haka ne wasu fusatattun matasa, da ake zargin masu goyon bayan ɗan majalisar ne, suka tarwatsa taron, inda aka kekketa rigar mai gabatar da taron (MC), wanda ya tsira da ƙyar.
Majiyoyi sun bayyana cewa wannan shi ne taron farko da ya haɗa tsagin ɗan majalisa Tijjani Jobe da na Engr. Abba Ganduje, waɗanda suka fafata a zaɓen 2023 kuma ke cikin rikicin siyasa tun daga wancan lokaci.
Haka kuma, wannan ne karo na farko da ‘yan siyasar yankin daga bangarorin Kwankwasiyya da Gandujiyya suka zauna a waje guda.
Daga cikin manyan mahalarta taron akwai masu neman kujerar majalisar tarayya, Barr. Munir Dahiru Maigari, tsohon Shugaban Karamar Hukumar Rimingado Dr.
Jinaidu Yakubu Tofa, Engr. Abba Ganduje, da kuma Babban Daraktan Yaɗa Labaran Gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, wanda ya halarci taron ta hanyar wayar tarho.
Sauran jagororin jam’iyyar da suka halarta sun haɗa da Malam Sani Tofa, Mai Bai wa Gwamna Shawara kan Ayyuka na Musamman, tsofaffin Kwamishinonin Ayyuka na Kano – Engr
Hamisu Lambu, Shehu Haruna Lambu da Idris Garba Unguwar Rimi, tsohon Kwamishinan Kasa Muhammad Nadu Yahaya, Farfesa Nura Yaro Dawakin Tofa, Farfesa Kabiru Dungurawa, da tsohon Shugaban Hukumar Yaƙi da Rashawa ta Kano, Barr. Muhyi Magaji Rimingado, tare da sauran manyan ‘yan siyasa da dama.
Har zuwa lokacin haɗa wannan labari, shugabannin jam’iyyar APC a jihar Kano ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.



