Labarai

Hatsarin Mota Ya Jikkata Akalla ‘Yan Jarida 14 a Bauchi

Aƙalla ‘yan jarida 14 daga kafafen watsa labarai daban-daban ne suka jikkata a ranar Juma’a sakamakon wani hatsarin mota da ya faru yayin da suke rangadin duba ayyukan da Hukumar Raya Arewa maso Gabas (NEDC) ke gudanarwa a Jihar Bauchi.

‘Yan jaridan na cikin tawagar NEDC da ke rangadin duba ayyukan da aka kammala domin miƙa su ga Gwamnatin Jihar Bauchi, lokacin da hatsarin ya faru a kan hanyar Yashi zuwa Yelwan Duguri, a Ƙaramar Hukumar Alkaleri.

Rahotanni sun nuna cewa da dama daga cikin ‘yan jaridan sun samu munanan raunuka, inda aka fara kai su Asibitin Yelwan Duguri domin samun agajin gaggawa, kafin daga bisani a mayar da waɗanda suka fi muni zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH) da ke Bauchi.

Daga cikin kafafen watsa labaran da ‘yan jaridansu suka jikkata akwai Channels Television, Africa Independent Television (AIT), Nigerian Television Authority (NTA), da ARISE News.

Biyo bayan faruwar lamarin, manyan jami’an gwamnati da suka haɗa da Kwamishinan Yaɗa Labarai, Mai Bai wa Gwamna Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai, Shugaban Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) reshen Jihar Bauchi, da Daraktan Yaɗa Labarai na Gidan Gwamnati, sun kai ziyara asibiti domin duba halin da ‘yan jaridan ke ciki.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button