Manajan Hikima Radio Abubakar Isa Dandago, Ya Yi Murabus

Babban Manajan gidan rediyon Hikima Radio da ke Jihar Kano, Abubakar Isa Dandago, ya yi murabus daga mukaminsa tare da fara aiki nan take.
Dandago ya bayyana hakan ne cikin wani saƙo da ya aika kai tsaye ga Independent Post a ranar Alhamis, inda ya ce dalilan murabus ɗinsa na da alaƙa da lamurra na kansa.
A cewarsa, “Ina amfani da wannan dama ne wajen sanar da abokan aiki na da kuma shugabancin gidan rediyon cewa na yi murabus daga mukamina na Babban Manaja.
Ina roƙon Allah Ya ci gaba da shiryar da mu a dukkan shawarwarin da muke yankewa.”
Ya ƙara da cewa duk da cewa matakin ya zo masa da raɗaɗi, amma ya yi imanin cewa shi ne daidai kuma ya zo a lokacin da ya dace.
Dandago ya nuna godiyarsa ga abokan aikinsa bisa goyon baya da haɗin kai da suka ba shi a tsawon lokacin da ya shafe yana aiki, tare da yaba wa masu mallakar gidan rediyon bisa damar da suka ba shi na yin hidima a wannan matsayi.
A ƙarshe, ya nemi afuwa daga duk wanda ya taɓa ɓata wa rai, ko da kuwa cikin sani ko rashin sani.




