Labarai

Rukayya Muhammad Ta Ajiye Aikinta a Arewa24 Domin Bunƙasa Harkokinta na Kasuwanci

Rukayya Muhammad, wadda ke rike da muƙamin shugabar sashin kula da shafukan sada zumunta a gidan talabijin na Arewa24, ta ajiye aikinta da tashar.

Rukayya ta bayyana hakan ne ta cikin wani rubutu da ta wallafa a shafinta na X, inda ta ce ta ɗauki wannan mataki ne domin bin burinta na rayuwa da kuma bunƙasa harkokinta na kasuwanci.

A cewarta, ta zaɓi ci gaba da ƙwarewa da haɓaka kanta, maimakon ci gaba da kasancewa a yanayin aiki da ta saba, tana mai bayyana kanta a matsayin mutum mai aiwatar da aiki, ba wai mai magana kawai ba.

Rukayya ta ƙara da cewa tana aiki ne wajen faɗaɗa kasuwancinta ta kafafen sada zumunta, tare da kafa wani kamfani da ke ba da sabis na gina suna da martabar kamfanoni da mutane (branding da dabarun talla).

Ta bayyana kanta a matsayin mace ta farko a Arewa da ta mallaki irin wannan kamfani.

Ta ce matakin da ta ɗauka ya yi daidai da burinta na neman ci gaba da bunƙasa rayuwarta ta aiki, tare da ƙudirin cimma manyan nasarori a fagen kasuwanci.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button