Mata Ta Kai Ƙara Kotun Shari’ar Musulunci Bisa Zargin Yi Mata Asiri da Hana Ta Aure Shekaru 11

matar mai suna Sadiya Abubakar Sani ta kai ƙara gaban Kotun Shari’ar Musulunci da ke Fagge ’Yan Alluna a Jihar Kano, inda take zargin tsohon mijinta da kuma wani malami da haɗa baki wajen yi mata asiri, wanda ta ce ya hana ta yin aure tsawon shekaru 11.
Rahotanni sun nuna cewa ’yan sanda ne suka gurfanar da Abubakar Hassan da Auwal Yusuf a gaban kotun bisa zargin haɗa baki da aikata asiri, a zaman kotun da Mai shari’a Mustapha Ashiru ya jagoranta.
A yayin zaman, an karanta wa waɗanda ake tuhuma zargin da ake yi musu, inda dukkaninsu suka musanta aikata laifukan da aka jingina musu.
Mai gabatar da ƙara ya roƙi kotu da ta ba shi ƙarin lokaci domin gabatar da shaidu da hujjoji da za su tabbatar da zargin da ake yi wa mutanen biyu.
Bayan sauraron ɓangarorin biyu, kotun ta bayar da belin waɗanda ake tuhuma, tare da ɗage shari’ar zuwa ranar 30 ga watan Maris, 2026, domin ci gaba da sauraron shari’ar.




