’Yan Sanda Sun Kama Shahararren Ɗan Daba Auwalu Dan Daba

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta sanar da cafke wani shahararren ɗan daba mai suna Auwalu Ali, wanda aka fi sani da “Auwalu Dan Daba”, a ranar 31 ga Janairun 2026 a unguwar Dorayi da ke cikin birnin Kano.
A cewar rundunar, an kama Auwalu ne bayan samun sahihin bayanan sirri, inda jami’an ‘yan sanda na Dorayi Division suka gudanar da sumame suka cafke shi.
Ana zargin Auwalu da jagoranci da shirya ƙungiyoyin daba da ke kai hare-haren fashi da ta’addanci ga jama’a a sassan jihar Kano.
A wani lamari na daban kuma, jami’an ‘yan sanda na Sharada Division sun kai ɗauki bayan samun kiran gaggawa daga Sharada Quarters, inda ake zargin wani ɗan fashi da makami ya gamu da ajalinsa bayan da fusatattun mutane suka yi masa dukan kawo wuƙa, sakamakon wani hari da ya kai wanda ya jikkata wata mata .
An garzaya da waccan mata zuwa Asibitin Murtala Mohammed domin ceto ranta.
A yayin kokarin ceton rayuwarta, wani jami’in ɗan sanda ya nuna jarumta da sadaukarwa ta hanyar ba da jininsa, lamarin da ya taimaka wajen ceto rayuwar waccan mata.
Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, PhD, sfipma, mnim, mnips, masis, ya yabawa jami’an da suka nuna jajircewa da sadaukarwa wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma, musamman wannan jami’in da ya ba da jininsa domin ceton rai.
Ya kuma gode wa al’ummar jihar Kano bisa ci gaba da ba rundunar goyon baya da haɗin kai.



