Sanata Kwankwaso Bai Sanya Sharaɗi Na Komawa APC Ba – Kwankwasiyya

Ƙungiyar Kwankwasiyya ta yi watsi da rahotannin da ke yaɗuwa musamman a shafukan sada zumunta, waɗanda ke iƙirarin cewa jagoran ƙungiyar, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya saka sharaɗi na komawa jam’iyyar APC.
A cewar ƙungiyar, wasu rahotanni sun rika nuna cewa Kwankwaso na shiga tattaunawa da jiga-jigan APC tare da gindaya wasu sharuɗa domin sauya sheƙa daga jam’iyyarsa ta NNPP zuwa APC.
Sai dai a cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, Kwankwasiyya ta bayyana matuƙar damuwa kan yawaitar irin waɗannan rahotanni, tana mai cewa ba su da tushe balle makama, kuma an ƙirƙire su ne domin ruɗar da al’umma.
Sanarwar ta jaddada cewa Sanata Kwankwaso bai taɓa shiga wata tattaunawa, ganawa ko shawarwari da jam’iyyar APC, Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ko wani daga cikin wakilansu ba dangane da batun sauya sheƙa.
“Babu wata hujja ko shaida da ke goyon bayan waɗannan zarge-zarge da ake yaɗawa,” in ji sanarwar.
Ƙungiyar ta kuma yi kakkausar suka ga wasu kafafen watsa labarai da masu sharhi kan siyasa, tana mai cewa abin takaici ne a rika wallafa zarge-zarge masu nauyi ba tare da yin cikakken bincike ko neman jin ta bakin wanda abin ya shafa ba.
Kwankwasiyya ta bayyana cewa ganawar ƙarshe da ta faru tsakanin Kwankwaso da Shugaba Tinubu ita ce a watan Janairun 2024, inda ba a tattauna ko sauya jam’iyya ko wata yarjejeniya ta siyasa ba.
Sanarwar ta ƙara da cewa hulɗar Kwankwaso da shugabanni daga jam’iyyu daban-daban abu ne na al’ada a tsarin dimokuraɗiyya, kuma bai kamata a juya hakan zuwa labaran bogi ba.
A ƙarshe, ƙungiyar Kwankwasiyya ta bayyana cewa tana kallon waɗannan rahotanni a matsayin yunƙurin ɓata suna da rage tasirin Kwankwaso a siyasar ƙasa, tare da kira ga ƴan Najeriya da su yi watsi da duk wani labari na ƙarya da ake yaɗawa a kansa
bbc




