Labarai

DANAGUNDI: DOLE AMINU ADO BAYER0 YA CI GABA DA ZAMA SARKIN KANO

Alhaji Aminu Babba Ɗanagundi, Sarkin Dawaki Babba kuma ɗaya daga cikin masu naɗa sarki a Masarautar Kano, ya jaddada cewa dole ne Aminu Ado Bayero ya ci gaba da zama Sarkin Kano, yana mai cewa duk wani yunƙuri na cire shi ta hanyar yarjejeniyar siyasa abu ne da ba zai taɓa yiwuwa ba.

 

Ɗanagundi, wanda ke ƙalubalantar Gwamnatin Jihar Kano a kotu kan soke dokar masarauta da kuma cire Sarkin Kano, ya bayyana wa jaridar Weekend Trust cewa lamarin yanzu haka yana gaban Kotun Ƙoli.

 

Ya yi watsi da ra’ayoyin da ke neman warware rikicin ta hanyar sasantawa a wajen kotu, yana mai cewa irin wannan hanya ba za ta kawo adalci ba.

 

A cewarsa, marigayi Sarkin Kano, Ado Bayero, ya yi sarauta na sama da shekaru 50 ba tare da aikata wani laifi da zai sa a tube shi daga karagar mulki ba.

 

Alhaji Aminu Babba Ɗanagundi ya ƙara da cewa ya shigar da ƙarar ne domin kare haƙƙoƙinsa na doka, yana mai nuni da cewa soke dokar masarauta ya shafe shi kai tsaye, ganin matsayinsa na ɗaya daga cikin masu ruwa da tsaki a harkar masarauta.

 

Sai dai, duk da tsayuwar dakan da ya nuna, Ɗanagundi ya amince cewa hukuncin ƙarshe na warware rikicin masarautar Kano yana hannun kotu, inda ya ce zai mutunta duk hukuncin da doka ta bayar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button