Labarai

’Yan Sanda Sun Kama Ma’aurata Kan Zargin Kitsa Garkuwa da Kansu a Legas

Rundunar ’yan sandan jihar Legas ta cafke wasu ma’aurata, Fred da matarsa Goodness, bisa zargin kitsa garkuwa da kansu tare da karɓar kuɗin fansa har Naira miliyan 10 daga dangi da abokansu.

Binciken Jaridar Aminiya ya nuna cewa ma’auratan sun ƙirƙiri labarin sacewar ne a ranar 7 ga watan Janairu, da nufin tara kuɗaɗen da mijin zai yi amfani da su wajen komawa ƙasar Amurka, sakamakon matsin tattalin arziƙi da rashin tallafin kuɗi.

Wani jami’in ’yan sanda da ya buƙaci a sakaya sunansa ya shaida wa Aminiya a ranar Alhamis cewa ma’auratan sun tuntuɓi ’yan uwansu da abokansu, inda suka yi ikirarin cewa wasu mutane sun sace su tare da neman kuɗin fansa.

Jami’in ya bayyana cewa ma’auratan sun tsara karɓar kuɗin ne a wata makaranta da ke yankin Cappa, Mushin, inda jami’an tsaro suka sa ido domin bibiyar lamarin.

“Mun lura da matar ta shiga wurin ita kaɗai da farko, daga bisani sai mijin ya iso. Amma abin ya ba mu shakku ne lokacin da suka fito tare da jaka.

Bayan mun bincika jakar, mun gano kuɗin fansa a ciki, wanda hakan ya sa aka kama su nan take,” in ji jami’in.

A yayin tambayoyi, matar ta amsa laifinta inda ta bayyana cewa ita ce ta shawarci mijinta su aiwatar da wannan shiri domin su samu kuɗin tafiya.

Rundunar ’yan sanda ta ce bincike na ci gaba da gudana, kuma za a gurfanar da ma’auratan a gaban kotu da zarar an kammala binciken.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button