Turkiyya Na Neman Haɓaka Cinikayya da Najeriya Zuwa Dala Biliyan 5 – Shugaba Erdogan

Shugaban Ƙasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya bayyana cewa ƙasarsa na da burin daga darajar cinikayya da Najeriya zuwa dala biliyan 5, yana mai cewa tuni aka fara tattaunawa domin cimma wannan buri.
Shugaba Erdogan ya bayyana hakan ne a ranar Talata a birnin Ankara, yayin taron manema labarai na haɗin gwiwa da Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, a lokacin ziyara ta musamman (State Visit) da shugaban Najeriya ke yi a ƙasar Turkiyya.
A halin yanzu, darajar cinikayya tsakanin ƙasashen biyu na kusan dala biliyan 2, inda Turkiyya ke fitar da jiragen sama da na helikwafta, injuna, ƙarafa, da sinadarai zuwa Najeriya.
A nata ɓangaren, Najeriya na fitar da danyen mai da kayayyakin noma zuwa Turkiyya.
Shugaba Erdogan ya ce kafa Kwamitin Tattalin Arziƙi da Cinikayya na Haɗin Gwiwa tsakanin ƙasashen biyu zai buɗe ƙofofi ga ƙarin jarin Turkiyya a Najeriya domin cimma burin da aka sanya.
Ya yaba da ƙudurin Shugaba Tinubu na bunƙasa tattalin arziƙin Najeriya, yana mai cewa halartar ministoci da manyan jami’ai a ziyarar alama ce ta ƙarfin niyyar siyasa.
“Mun yi cikakken nazari kan dangantakarmu da Shugaba Tinubu da tawagarsa, musamman a fannonin cinikayya, zuba jari, makamashi, ilimi da masana’antar tsaro. Mun amince da burin kai cinikayya zuwa dala biliyan 5 tare da tattauna matakan cimma hakan,” in ji Erdogan.
Shugaban Turkiyya ya kuma yaba da gyare-gyaren da Najeriya ke yi a ɓangaren makamashi, yana fatan haɗin gwiwa tsakanin Kamfanin Man Fetur na Turkiyya da abokan aikinsu na Najeriya zai samar da sakamako mai kyau.
Dangane da tsaro, Erdogan ya yi alƙawarin taimaka wa Najeriya wajen yaƙi da ta’addanci, yana mai nuni da ƙwarewar Turkiyya a irin wannan fagen.
“Ƙungiyoyin ta’addanci, musamman a yankin Sahel na Afirka, na barazana ga zaman lafiya. Muna tare da al’ummar Najeriya a yaƙinsu da ta’addanci ƙarƙashin jagorancin Shugaba Tinubu,” in ji shi.
A nasa jawabin, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gode wa Turkiyya kan shirinta na haɗin gwiwa wajen bunƙasa ’yanci, zaman lafiya da wadata a duniya. Ya jaddada muhimmancin gina tattalin arziƙi mai haɗa kowa, musamman masu rauni a cikin al’umma.
Shugaba Tinubu ya kuma bayyana cewa Najeriya za ta ci gaba da taka rawa wajen inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali a Afirka, duk da ƙalubalen tsaro da ake fuskanta a wasu sassan ƙasar.
A ƙarshen taron, jami’an ƙasashen biyu sun sa hannu kan yarjejeniyoyi guda tara, ciki har da yarjejeniyoyin tsaro, ilimi, hulɗar kafofin watsa labarai, kula da al’umma, da kafa Kwamitin Tattalin Arziƙi da Cinikayya na Haɗin Gwiwa.



