Majalisar Dattawan Najeriya Ta Fara Nazarin Gyaran Dokar Zaɓe ta 2022

Majalisar Dattawan Najeriya ta fara nazari kan ƙudirin gyara Dokar Zaɓe ta shekarar 2022, inda ta mayar da hankali kan wasu muhimman sassa da ake ganin suna buƙatar ƙarin gyare-gyare domin inganta sahihanci da gaskiya a tsarin zaɓen ƙasar.
Ƴan majalisar sun fara wannan aiki ne ta hanyar nazarin wasu takardu da shawarwari da Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Harkokin Zaɓe, Sanata Simon Lalong, ya gabatar, kafin a shiga muhawara a bainar jama’a.
Ƙudirin gyaran dokar ya ƙunshi batutuwa da dama da suka haɗa da hana yin rajista a jam’iyyun siyasa fiye da ɗaya, daƙile sauya sheƙa bayan zaɓen fidda gwani, da kuma tanadin hukunci ga duk masu karya dokokin zaɓe.
A zaman majalisar, ‘yan majalisar sun amince da buƙatar janye wasu sassan ƙudirin da aka riga aka amince da su a watan Disambar 2025, domin a sake duba su cikin tsanaki, la’akari da tasirinsu ga tsarin dimokiraɗiyya.
Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya jaddada muhimmancin yin cikakken nazari kan ƙudirin, duk da cewa Majalisar Wakilai ta riga ta amince da shi.
Ya bayyana cewa dokar zaɓe na da matuƙar muhimmanci, musamman yayin da ake shirin gudanar da zaɓe a ƙasar, don haka ya zama wajibi a yi taka-tsantsan domin kauce wa rikice-rikicen shari’a bayan zaɓe.
Kwamitin Majalisar Dattawa ya bayyana cewa aiwatar da gyaran dokar zai taimaka wajen ƙarfafa gaskiya da adalci a tsarin zaɓe, da ƙara amincewar jama’a da sakamakon zaɓe, tare da faɗaɗa damar masu kaɗa ƙuri’a da kuma ƙarfafa ikon Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) wajen daƙile maguɗin zaɓe.




