NESREA: ’Yan Najeriya Na Shan Sama da Lita Biliyan 2.5 na Ruwan Leda a Duk Shekara

Hukumar Kula da Tsaftace Muhalli ta Ƙasa (NESREA) ta bayyana cewa a duk shekara, ’yan Najeriya na shan sama da lita biliyan 2.5 na ruwan leda, wanda kamfanoni fiye da 32,000 ke samarwa a faɗin ƙasar.
Shugaban hukumar, Innocent Barikor, ne ya bayyana hakan a yayin wani taro na GEF Child Project 11193, da aka gudanar a ranar Talata a Abuja.
Taron, mai taken “Samar da hanyoyin kawar da amfani da leda a Najeriya”, an shirya shi ne domin lalubo hanyoyin da za su rage amfani da ruwan leda, tare da tabbatar da cewa jama’a na samun ruwa mai tsafta ba tare da jawo illa ga muhalli ba.
Barikor ya bayyana cewa wannan zama zai taimaka matuƙa wajen rage matsalolin muhalli da ke da alaƙa da yawaitar amfani da ledoji a ƙasar.
Ya ce duk da cewa ƙirƙirar fasahar yin ruwa a leda ta taimaka wajen sauƙaƙa samun ruwa mai tsafta ga jama’a, hakan ya zo da mummunar illa ga muhalli.
Daga cikin illolin da ruwan leda ke haifarwa, Barikor ya ambaci toshe hanyoyin ruwa, haɗarin cututtuka ga lafiyar al’umma, da kuma jawo ambaliyar ruwa, baya ga sauran matsalolin muhalli da ke barazana ga rayuwar jama’a.
Shugaban NESREA ya jaddada cewa tattauna hanyoyin samar da ruwa mai tsafta ba tare da cutar da muhalli ba, abu ne mai matuƙar muhimmanci a wannan lokaci.
Ya ƙara da cewa shirin Global Environment Facility (GEF) Child Project 11193 zai taimaka wajen gano ingantattun hanyoyin zubar da shara da ledoji yadda ya kamata.
A cewarsa, wannan mataki na daga cikin manyan manufofin NESREA na kare muhalli da tabbatar da kyakkyawar makoma ga al’umma da ƙasar Najeriya baki ɗaya.




