Babbar Kotun Tarayya Ta Aike Shugaban KANSIEC na jihar Kano Gidan Yari

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta bayar da umarnin tsare Shugaban Hukumar Zaɓe ta Jihar Kano (KANSIEC), Sani Malumfashi, tare da Sakataren hukumar, Anas Muhammed Mustapha, da kuma jami’in kula da lissafin kuɗade, Ado Garba, a gidan yari na Kuje.
Kotun ta ɗauki wannan mataki ne bayan gurfanar da su kan zargin hannu a wata babbar badakalar almundahanar kuɗi da ta kai Naira biliyan ɗaya (₦1bn).
A yayin zaman kotun, dukkansu sun musanta zarge-zargen da ake yi musu, suna mai cewa ba su aikata laifin da ake tuhumar su da shi ba.
Mai shari’a ya bayyana cewa kotun za ta ci gaba da tsare su a gidan yari har sai an saurari buƙatar belin su a hukumance.
Haka kuma, kotun ta ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 28 ga Janairu, 2026, domin sauraron buƙatar belin.




