Sojojin Operation HADIN KAI Sun Kama Tsohuwa Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi ga Boko Haram a Borno

Dakarun rundunar haɗin gwiwa ta Arewa maso Gabas, Operation HADIN KAI, sun cafke wata mata ‘yar kimanin shekaru 65 bisa zargin safarar miyagun ƙwayoyi ga ‘yan ƙungiyar Boko Haram da ke kai hare-hare a wasu sassan Jihar Borno.
An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na rundunar, Laftanar Kanar Sani Uba, ya fitar, inda ya ce an kama wadda ake zargi a ƙaramar hukumar Askira Uba ta Jihar Borno, a ranar 23 ga Janairun 2026, yayin wani samame da rundunar ta kai bisa bayanan sirri da ta tattara.
A cewar sanarwar, ana zargin matar da zama babbar mai samar da tabar wiwi ga ‘yan Boko Haram da ke aiki a yankuna daban-daban da suka haɗa da Askira Uba, Rumirgo, Gwahi, Wamdiyo, Uvu da kuma Gaya.
Binciken farko ya nuna cewa wadda ake zargi na samo tabar wiwin ne daga ƙaramar hukumar Sarti Baruwa da ke Jihar Taraba.
Haka kuma, an kama ta da ƙunshin ganyen wiwi guda 14, masu nauyin kimanin kilogiram 30.
“Wadda ake zargi na nan a tsare yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike domin gano tare da wargaza hanyoyin da ake amfani da su wajen safara da rarraba miyagun ƙwayoyi,” in ji sanarwar.
Rundunar Operation HADIN KAI ta jaddada aniyarta ta ci gaba da yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi da kuma duk wani nau’i na tallafa wa ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso Gabas.




