GCHN Reshen Dawakin Tofa Ta Gudanar da Bita Kan Kare ‘Yancin Dan Adam

Kungiyar Global Community for Human Rights Network (GCHN) reshen karamar hukumar Dawakin Tofa, Jihar Kano, ta gudanar da taron bita karo na biyu ga jami’anta a ranar Lahadi, 25 ga Janairu, 2026, domin ƙara wayar da kai da ilimantar da su kan aikinsu na kare ‘yancin dan adam.
Barista Muhammad Tasi’u Abdullahi ne ya jagoranci bitar mai taken “Me Ne Ne Aikin Kungiyoyin Kare ‘Yancin Dan Adam”, inda ya bayyana cewa abu ne mai matuƙar muhimmanci jami’an kungiyoyin su san ma’anar ‘yancin dan adam kafin su fara aikin kare al’umma daga take hakkin su.
Ya ce:
“Aikin farko na kungiyoyin kare ‘yancin dan adam shi ne ilmantar da al’umma kan menene ‘yancin dan adam, ta hanyar shirya taruka na fadakarwa, sannan a bi duk wanda aka ko ake yunkurin take masa ‘yancin.”
Barista Tasi’u ya bayyana cewa aikin kungiyar ya haɗa da:
Bibiyar duk wanda aka take hakkin sa,
Ba shi tallafi ko daukar lauyan da zai kare shi,
Matsawa gwamnati wajen dakile keta ‘yancin dan adam,
Hada kai da hukumomi don kare ‘yancin dan adam,
Adana bayanan laifukan keta ‘yancin dan adam a koda yaushe.
Horon bitar ya gudana ne a makarantar Dawakin Tofa Special Primary School, karkashin jagorancin Malam Yusif Garba Tauwa, koordinatorin GCHN reshen karamar hukumar Dawakin Tofa
Horon ya samu halartar jami’an kungiyar da dama, inda aka tattauna hanyoyin ƙarfafa aikinsu wajen kare hakkin al’umma bisa ka’ida da doka.




