Sojojin Sun Musanta Zargin Tafiyar Hawainiya Kan Harin Kurmin Wali a Kaduna

Rundunar Sojin Najeriya ta musanta zargin cewa tana tafiyar hawainiya wajen kai ɗauki bayan harin da aka kai a yankin Kurmin Wali da ke jihar Kaduna, inda aka sace masu ibada sama da 100 a ranar Lahadin da ta gabata.
Wasu daga cikin al’ummar ƙaramar hukumar Kajuru sun yi zargin cewa jami’an tsaro sun nuna sakaci, tare da cewa ba a yi gaggawar kai ɗauki domin kuɓutar da masu ibadar da aka sace ba.
Sai dai shalkwatar tsaron ƙasa ta musanta waɗannan iƙirari, tana mai bayyana cewa ana ci gaba da gudanar da ayyukan tsaro domin ganin an ceto waɗanda abin ya shafa cikin gaggawa.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai na Rundunar Sojin Najeriya, Manjo Janar Michael Onoja, ya fitar, inda ya bai wa al’umma tabbacin cewa za a ceto waɗanda aka sace cikin ƙoshin lafiya.
“Saɓanin iƙirarin da ake yi na tafiyar hawainiya, Rundunar Sojin Ƙasa tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro na ci gaba da gudanar da ayyukan leƙen asiri a dazukan da ‘yan bindiga ke fakewa,” in ji sanarwar.
Rundunar Sojin Najeriya ta kuma jaddada aniyarta ta kare rayuka da dukiyoyin jama’a, tare da sha alwashin ganin an sake haɗa waɗanda harin Kurmin Wali ya rutsa da su da iyalansu a mafi ƙanƙantar lokaci.



