Labarai

Malami Ya Zargi DSS da Tauye Masa Haƙƙin Kare Kansa a Gaban Kotu

Tsohon Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya, Abubakar Malami (SAN), ya zargi Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) da aikata wasu matakai da ya ce suna tauye masa haƙƙinsa na samun adalci a shari’ar da ake yi masa.

Malami ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Mohammed Bello Doka, ya sanya wa hannu, inda ya ce hukumar DSS na ci gaba da hana shi ganawa da lauyoyinsa, lamarin da ke kawo masa cikas wajen kare kansa daga zarge-zargen da ake yi masa.

 

A cewarsa, matakan da DSS ke ɗauka na nuni da yunƙurin tauye doka da oda, inda ya bayyana su a matsayin wani yunkuri na yi wa doka zagon ƙasa.

 

“Waɗannan abubuwan da ke faruwa suna nuna wani tsari na kama mutum kafin kammala bincike, tare da neman tattara hujjoji bayan tsarewa, al’amari da ya saɓa wa doka da kuma ‘yancin da kundin tsarin mulki ya tanada,” in ji sanarwar.

 

Sanarwar ta ƙara da cewa kama Malami ya zo ne a daidai lokacin da yake buƙatar cikakken damar kare kansa a shari’ar da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ke yi masa a gaban Babbar Kotun Tarayya.

 

Sai dai Malami ya jaddada aniyarsa ta kare kansa bisa doka a gaban kotu, yana mai bayyana cewa ba zai yi ƙasa a gwiwa ba wajen neman adalci.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button