Siyasa

Gwamnatin Kano Ta Gargaɗi Magoya Bayan Gwamna Abba Kan Suka ko Cin Mutuncin Kwankwaso

Gwamnatin Jihar Kano ta yi gargaɗi ga magoya bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf da su guji cin mutunci ko sukar jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, tana mai cewa duk wanda ya saɓa wa wannan umarni zai fuskanci hukunci bisa doka.

Gargaɗin ya fito ne a cikin wata sanarwa da Babban Daraktan Yaɗa Labarai na Fadar Gwamnati, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Asabar, 24 ga Janairu, 2026.

A cewar sanarwar, sauyin siyasa ba ya hana girmamawa, inda gwamnatin ta jaddada cewa ya zama wajibi a ci gaba da mutunta Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso duk da duk wani sauyi da aka samu a fagen siyasa.

Sanarwar ta kuma yi kira ga magoya bayan gwamnan da su nuna ladabi, kamun kai da ɗabi’ar siyasa mai kyau, tare da guje wa kalaman da ka iya haifar da tashin hankali ko rarrabuwar kawuna.

 

Gwamnatin jihar ta jaddada aniyarta ta tabbatar da zaman lafiya da tsaro a faɗin Kano, tana mai gargaɗin cewa ba za ta lamunci duk wani abu da zai iya kawo cikas ga zaman lafiyar al’umma ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button